Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ba ta yi mamakin janyewar Amurka daga yarjejeniyar makamai masu linzami ba
2019-12-13 20:09:39        cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Hua Chunying ta bayyana cewa, janyewar da Amurka ta yi daga yarjejeniyar dakile makamai masu linzami masu cin matsakaicin zango abu ne da Amurkar ta shirya, kuma hakan na kara tabbatar da shirin Amurka na kera makamai masu linzami da ma yadda sojojinta za su kara fita daga dangi.

Rahotanni na cewa, ma'aikatar tsaron Amurka ta tabbatar da cewa, Amurka ta yi gwajin makami mai linzami a wannan rana. Wannan shi ne karo na biyu da bangaren Amurkar ke gwajin makami mai linzami bayan janyewa daga yarjejeniya a wannan shekara.

Hua Chunying ta yi nuni da cewa, ya kamata al'ummomin kasa da kasa su bude idonsu su kuma fahimci makircin Amurka a neman ware kanta da ma yin babakere a tsarin tsaron makamai na kasa da kasa. A don haka, bangaren kasar Sin ya bukaci bangaren Amurka da ya yi watsi da tunanin yakin cacar baka da ma wasa da hankali, maimakon haka, kamata ya yi ya mayar da hankali wajen tabbatar da zaman lafiya da daidaito a duniya, sannan ta shiga a dama da ita a kokarin da ake na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a shiyya-shiyya da ma duniya baki daya.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China