Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kebe mutane 70 a sanadiyyar barkewar zazzabin lassa a Nijeriya
2020-02-19 10:29:21        cri
Gwamnatin jihar Kano dake arewa maso yammacin Nijeriya, ta ce an kebe kimanin mutane 70 da suka yi mu'amala da wadanda suka kamu da zazzabin lassa a jihar, domin ba su kulawa.

A cewar kwamishinan lafiya na jihar, Aminu Tsanyawa, mutanen 70 na daga cikin mutane 390 da aka kebe tun da farko, saboda mu'amalar da suka yi da wadanda suka kamu da cutar.

Ya kuma shaidawa manema labarai a Kanon cewa, an duba lafiyar sama da mutane 300, kuma kawo yanzu an sallame su. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China