Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Najeriya ya ziyarci wadanda harin Boko Haram ya rutsa da su a jihar Borno
2020-02-13 11:31:22        cri
A jiya ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kai ziyara a jihar Borno, don jajantawa wadanda harin Boko Haram na farkon wannan mako ya rutsa da su, inda a kalla mutane 30 suka rasa rayukansu.

Jirgin saman dake dauke da shugaban, ya sauka ne da yammacin jiya a sansanin mayakan sama dake Maiduguri, a kan hanyarsa ta dawowa daga taron kolin kungiyar tarayyar Afirka (AU) da aka gudanar a birnin Addis Abeba na kasar Habasha a karshen makon jiya, inda nan take ya fara ziyarar aiki a jihar.

Mai Magana da yawun shugaban ya shaidawa kamfanin dillancin labaru na Xinhua na kasar Sin cewa, shugaban ya kai ziyarar ce, don yi wa iyalan wadanda harin ya rutsa da su ta'aziya, ya kuma gana da jami'an gwamnatin jihar kan lamarin.

Gwamnan jihar Borno Babagan Zulum ya tabbatar a ranar Litinin cewa, a kalla mutane 30 ne aka kashe, a harin da ake zaton mayakan Boko Haram ne suka kaddamar ranar Lahadi da dare.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China