Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babu abun da zai rusa dangantakar Sin da Tanzania
2019-09-28 15:51:53        cri
Tsohon Firaministan Tanzania Salim Ahmed Salim, ya ce dangatakar Sin da Tanzania za ta ci gaba da kasancewa mai karfi, ba tare da la'akari da sauye-sauyen yanayin duniya ba.

Cikin wata rubutacciyar hira da ya yi da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, Salim Ahmed Salim, ya ce dangantakar dake tsakanin kasashen biyu ta musammam ce da ta jure gomman shekaru.

Ya ce an raya dangantakar ne bisa hangen nesa da imanin cewa, kasar ce kadai ke da karfi da damar inganta ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al'ummarta.

Ya kara da cewa, dangantaka ce ta abota da aminci. Kuma cikin shekarun da suka gabata, kasar Sin ta bada gagarumar gudunmuwa ga ci gaban nahiyar Afrika, yana mai cewa ta kasance muhimmiya wajen raya tattalin arzikin nahiyar, inda ya yi fatan Sin da kasashen Afrika, za su kara inganta dangantakarsu domin taimakawa nahiyar cimma burinta na sauya fasalin tattalin arziki.

Ya ce ya yi ammana dangantaka tsakanin al'ummar Tanzania da takwarorinsu na kasar Sin, za ta taka rawa a fannin samar da ci gaba. Yana mai cewa, za a ci gaba da kasancewa tare. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China