Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin wadanda suka mutu sanadiyyar mamakon ruwan sama a Tanzania ya kai 44
2019-10-28 10:30:38        cri
Wasu karin mutane 4 sun mutu sanadiyyar ruwan sama mai karfi a Tanzania, wanda ya kawo adadin wadanda suka mutu sanadiyyar ruwan saman zuwa 44.

Edward Bukombe, shugaban 'yan sandan yankin Tanga, ya shaidawa Xinhua ta wayar tarho cewa, wasu karin mutum 4 sun mutu, ciki har da yara 3, saboda ambaliyar ruwa a sassa daban-daban na gundumar Handeni.

Ya ce masu aikin ceto sun gano gawarwaki 4 a wurare daban daban na gundumar Handeni.

A ranar Asabar ne jami'in dan sandan ya ce adadin wadanda suka mutu sanadiyyar mamakon ruwan sama da ake yi a kasar ya tashi daga 30 zuwa 40.

Edward Bukombe ya kara da cewa, ruwa ya tafi da wata mota mai dauke da mutane 10 da asubahin ranar Asabar, bayan direban ya yi kokarin wucewa ta cikin kogin da ya tumbatsa a yankin Handeni, wanda ya kawo adadin wadanda suka mutun zuwa 40.

A ranar Alhamis ne hukumar kula da yanayi ta kasar, ta fitar da gargadi na 3 cikin wata guda, tana mai cewa ana tsammanin samun ruwan sama mai karfi a wasu sassan kasar da za a shafe kwanaki 5 ana yi tun daga ranar Jumma'a. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China