Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Trump da Erdogan sun tattauna batun rikicin Syria da Libya ta wayar hannu
2020-02-17 14:22:32        cri
Shugaban kasar Amurka Donald Trump ya tattauna da takwaransa na kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan a ranar Asabar game da batun rikicin kasashen Syria da Libya, a cewar wata sanarwa daga fadar White House.

A tattaunawar tasu, Trump ya bayyana damuwa game da rikicin yankin Idlib, wanda ya kasance yanki na baya-bayan a Syria dake karkashin ikon 'yan tawaye, ya bukaci a yi amfani da matakan siyasa wajen warware rikicin kasar Syria, a cewar fadar ta White House.

Trump da Erdogan sun yi musayar ra'ayoyi game da yadda za'a kawo karshen rikicin yankin Idlib nan ba da jimawa ba.

Tun da farko a ranar Jumma'a, ma'aikatar harkokin tsaron Turkiyya ta ce an kashe dakarun sojojin gwamnatin Syria 63 a yankin Idlib a wasu munanan hare-haren da Turkiyyar ta kaddamar, kamar yadda wasu bayanai daga majiyoyi daban daban suka ayyana.

Sai dai a wannan rana dakarun sojojin Rasha sun yi watsi da ikirarin da Ankara ta yi kana sun yi gargadin cewa wannan zargi ne Turkiyya ke yi kuma babu abin da hakan zai haifar sai lalata yanayin da ake ciki kuma zai yi sanadiyyar daukar matakan gaggawa wadanda ba za su dace da muradun da Rasha da Turkiyya suka cimma matsaya kansu ba.(Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China