Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka ta yi barzanar kakabawa Iraqi takunkumi, bayan kuri'ar da majalisar dokokin kasar ta kada dangane da Amurukar
2020-01-06 13:02:11        cri
Shugaban Amurka Donald Trump, ya yi barazanar kakabawa Iraqi takunkumai masu tsauri, bayan majalisar dokokin kasar da yaki ya daidaita, ta amince da kudurin dake neman gwamnati ta kori dakarun kasashen waje daga kasar.

Donald Trump ya shaidawa manema labarai jiya cewa, idan har Iraqi ta kori sojojin Amurka ba cikin yanayi na fahimtar juna ba, to Amurka za ta kakaba mata takunkuman da ba ta taba gani ba, wadanda za su sa a dauki takunkuman da aka sanyawa Iran a matsayin masu sauki.

Cikin wata sanarwar da ta fitar a jiya, ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce, Amurka ta yi takaicin matakin da majalisar Iraqi ta dauka.

Sanarwar ta kara da cewa, suna bukatar shugabannin Iraqi su yi nazarin muhimmancin dangantakar tattalin arziki da tsaro dake tsakanin kasashen biyu da kuma ci gaba da kasancewar dakarun kawancen kasashen na yaki da IS. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China