Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Trump ya ce yana son majalisar dattawan kasar ta hanzarta tattauna batun tsige shi
2019-12-20 12:32:57        cri

Shugaba Donald Trump na Amurka ya bayyana cewa, yana son majalisar dattawan kasar, ta hanzarta tattauna batun tsige shi, bayan da majalisar wakilan kasar ta kada kuri'ar tsige shi kan wasu ayoyin tuhume-tuhume guda biyu.

Trump ya wallafa a shafinsa na tweeter cewa, 'yan jami'iyyar demokirat ba su bi ka'ida a zauren majalisa ba, babu lauyoyi, babu shaidu, babu komai, yanzu kuma suna son su fadawa majalisar dattawa yadda za su yanke nasu hukuncin. Gaskiyar magana ita ce, ba su da wata shaida, ba su da abin da za su nuna. Ina son a hanzarta yanke hukunci.

Kuri'ar da majalisar wakilan ta kada ranar Laraba, ya sanya Trump zama shugaban Amurka na uku a tarihin da za a tsige, zai kuma fuskanci majalisar dattawa.

Da farko dai, majalisar wakilan ta kada kuri'a ne, kan zargin da ake yiwa shugaban na amfani da ikonsa ta hanyar da ba ta dace ba, sai zargi na biyu, game da kokarin hana majalisa yin aikin ta. Sai dai 'yan majalisar Republican baki daya sun yi watsi da wadannan tuhume-tuhume guda biyu.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China