Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tanzania na zaman makokin wadanda suka rasu a fashewar tankar mai
2019-08-11 16:23:31        cri
Shugaban kasar Tanzania John Magufuli ya sanar da zaman makokin kwanaki 3 a duk fadin kasar bayan fashewar wata tankar mai wacce ta kashe fiye da mutane 60 gami da raunata wasu 70 a birnin Morogoro na kasar a jiya Asabar, a cewar sanarwar da aka gabatar a yau Lahadi.

Ofishin watsa labarai na shugaban kasar ne ya gabatar da sanarwar a Dar es Salaam, cibiyar tattalin arziki ta kasar, an ce an fara zaman makokin ne tun daga jiya Asabar, kuma zai ci gaba har zuwa Litinin mai zuwa.

An kara bayyanawa a cikin sanarwar cewa, za a saukar da tutocin kasar dake wurare daban daban zuwa rabin sanda, yayin da ake zaman makokin, sa'an nan shugaba Magufuli zai tura firaministan kasar Kassim Majaliwa zuwa birnin Morogoro, domin ya halarci bikin jana'izar wadanda suka rasu, a madadin shugaban kasar.

A daren jiya, 'yan sandan kasar sun ce yawan mutanen da suka mutu ya karu zuwa 64, sakamakon fashewar tankar mai a Morogoro, dake da nisan kilomita 200 a yammacin birnin Dar es Salaam. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China