Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban jami'in WHO: Sin ta yi namijin kokari wajen yaki da cutar coronavirus
2020-02-16 16:27:56        cri

A jiya ne, babban direktan hukumar lafiya ta duniya wato WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya yi jawabi a gun babban taron tsaro na kasa da kasa a Munich na kasar Jamus, inda ya yabawa kasar Sin bisa namijin kokarin da take yi wajen yaki da cutar coronavirus, da hana yaduwar cutar, ya ce ya kamata kasa da kasa su nuna yabo gare ta.

Tedros ya jaddada cewa, yayin da ake tinkarar cutar, ya kamata kasa da kasa su yi hadin gwiwa, kana ya dace hukumomi daban daban dake cikin kasashen duniya su yi hadin kai, musamman kasashen da tsarin kiwon lafiyarsu ba shi da inganci don fuskantar kalubale. Ya yi kira da a bi tunani na gaske, kana kafofin watsa labaru su yi hadin gwiwa don hana yada jita-jita da kaucewa yada labaru marasa tushe. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China