Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin za ta tattauna da WHO don fayyace yanayin sabuwar cutar numfashi da ta bulla a kasar
2020-01-21 20:19:42        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Geng Shuang, ya ce Sin za ta halarci wani taro da kwamitin kasa da kasa mai lura da dokokin da suka jibanci kiwon lafiya ya kira, bisa gayyatar hukumar lafiya ta duniya WHO.

Kasashe mahalarta taron, da WHO, da sauran kwararru a fannin kiwon lafiya, za su yi musayar bayanai game da wannan cuta, tare da gudanar da binciken kimiyya, domin tabbatar da matsayin tasirin ta ga bil Adama.

Jami'in ya kara da cewa, Sin a shirye take, ta ci gaba da hadin gwiwa da sauran sassan duniya, wajen dakile yaduwar wannan cuta, tare da daukar matakan kandagarkin aukuwar annobar lafiya a mataki na shiyya shiyya, da na duniya baki daya.

A cewar Geng Shuang, gwamnatin kasar Sin na dora muhimmancin gaske, ga samar da kariya, da kawo karshen yaduwar sabuwar cutar ta numfashi, ta amfani da dukkanin matakan da suka wajaba. Za kuma ta yi hakan a bude, tare da kiyaye dukkanin dokoki da ka'idojin kariya na kasa da kasa.

Tuni dai Sin ta sanar da kasashe masu ruwa da tsaki, da hukumar WHO, da mahukuntan yankunan Hong Kong, da Macao da Taiwan, game da bullar wannan cuta a kan lokaci, kuma a karon farko ta gabatar da bayanai masu nasaba da kwayoyin halittar cutar. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China