Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanoni Ba Za Su Janye Daga Sin Saboda Cutar Numfashi Ba, In Ji Jim Rogers
2020-02-05 16:08:38        cri
Jim Rogers, wanda aka fi sani da "Sarkin Hajoji a Wall Street" na kasar Amurka ya bayyana cewa, ina jin mamaki kan wannan batu, ba na ganin cewa lamarin zai kasance gaskiya, ko da yake mai yuwa ne wasu sassa za su komawa kasashensu, amma a gani na, ba wanda zai bar kasar Sin ya koma gidajensu a kasar Amurka ko sauran kasashen duniya.

Ya ce kasar Sin tana aiwartar da matakan yaki da cutar numfashi yadda ya kamata, kuma sauran kasashen duniya su ma suna da irin wadannan matsaloli. A bara, mutanen Amurka guda dubu 80 sun rasu sakamakon kamuwa da mura, ko kamfanoni za su janye daga kasar Amurka sabo da wannan batu ne? Ana da irin wannan cuta a ko wace shekara. Shi ya sa ina jin mamaki kan abun da Wilbur Ross (ministan harkokin kasuwanci na kasarAmurka) ya fadi cewa, amma ba zan mai da hankali kan maganar tasa ba. Kana ban taba mai da hankali kan bullar cutar SARS ba.

Ko shakka babu, ya kamata mu kula da harkoki daban daban masu nasaba da haka, amma matsalar cutar SARS, matsala ce ta shekaru da dama da suka gabata, kasar Sin halin yanzu ba kamar a wancan lokacin take ba, kusan ba ta da bashi. Lallai yau ba jiya ba ce, yanzu, muna da abun da ya fi batun cutar muhimmanci a gabanmu. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China