Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin na amfani da mutum-mutumin inji wajen yaki da cutar Corona
2020-02-07 19:29:21        cri
Shugaban asibitin al'umma na lardin Guangdong dake yankin kudancin kasar Sin, Yu Xueqing, ya bayyana cewa, yanzu haka, kasar Sin tana kara amfani da mutum-mutumin inji a yakin da take yi da cutar numfashin da ta bulla a kasar.

Yu Xueqing ya ce, an dauki wannan mataki ne don hana yaduwar cutar. A halin yanzu asibitinsa na amfani da irin wadannan na'urori guda biyu, wajen jigilar kayayyaki a yankunan da ake killace masu fama da wannan annoba. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China