Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin ta dawo da mazauna lardin Hubei fiye da 1500 da ke ketare
2020-02-07 19:19:26        cri
Yu Biao, shugaban sashen kula da harkokin zirga-zirga na hukumar harkokin zirga-zirgar fasinja ta kasar Sin ya bayyana jiya Alhamis cewa, bayan barkewar annobar cutar numfashi, hukumar ta tura jiragen sama har sau 12 bisa taimakon ofisoshin jakadancin kasar Sin da ke kasashen ketare, don dawo da mazauna lardin Hubei fiye da 1500 wadanda suka yi yawo, kuma suka makale a katare. Nan gaba hukumar za ta ci gaba da tura jiragen sama don dawo da masu yawon shakatwa na kasar Sin da suka makale a wasu kasashen ketare. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China