Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Antonio Guterres da Tedros Ghebreyesus za su halarci taron AU karo na 33
2020-02-05 11:00:22        cri

Mukaddashin babban jami'in tsare tsare a ma'aikatar harkokin wajen kasar Habasha Gisila Shawel, ya ce babban magatakardar MDD Antonio Guterres, da babban daraktan hukumar lafiya ta duniya WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus, na cikin manyan jami'an da za su halarci taron gama gari na 33, na kungiyar tarayyar Afirka ta AU.

Mr. Shawel, ya ce jagororin biyu, na cikin manyan jami'ai da wakilan gwamnatocin Afirka da za su halarci taron na ranekun 21 ga watan Janairu zuwa 10 ga watan nan na Fabarairu, a hedkwatar kungiyar AU dake birnin Addis Ababa, fadar mulkin kasar Habasha. Taken taron dai shi ne "dakatar da amon bindiga: Samar da kyakkyawan yanayin bunkasa nahiyar Afirka ".

An dai tsara gudanar da taron shugabannin kasashe mambobin kungiyar karo 33 ne a ranekun 9 da 10 ga watan nan, kafin wannan kuma a bude taron gama gari na 36 a ranekun 6 da 7 ga wata, na majalissar zartaswar kungiyar ta AU, majalissar dake kunshe da ministocin kasashe mambobin AU.

Cikin bakin da za su halarci taron daga ketaren nahiyar hadda firaministan Canadia Justin Trudeau, da takwaransa na Norway Erna Solberg, da kuma shugabannin kasashen Afirka su 31. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China