Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta samu sabbin mutane 2,656 da aka tabbatar sun kamu da cutar coronavirus wasu 89 sun mutu
2020-02-09 15:55:33        cri
Hukumar kiwon lafiyar kasar Sin ta sanar a yau Lahadi cewa sabbin adadin mutanen da suka kamu da cutar numfashi ta coronavirus sun kai 2,656 kana adadin sabbin mutanen da suka mutu a sanadiyyar cutar sun kai 89, ya zuwa ranar Asabar daga fadin lardunan kasar 31 gami da rukunin sojoji ma'aikata masu ba da taimako a jihar Xinjiang.

Hukumar ta kara da cewa yawan sabbin mutanen da ake zaton sun kamu da cutar ya tasamma 3,916 ya zuwa ranar Asabar.

Kana ya zuwa ranar Asabar din yawan marasa lafiyar dake cikin matsanancin hali ya kai 87, yayin da aka sallami sabbin yawan mutane 600 bayan sun warke daga annobar.

Baki dayan adadin mutanen da suka kamu da cutar a fadin kasar Sin sun kai 37,198 ya zuwa karshen ranar Asabar, a cewar hukumar lafiyar, yayin da jimillar mutanen da annobar ta hallaka a fadin kasar ya kai 811.

Sai kuma majinyata 2,649 da aka sallama daga asibiti bayan sun warke daga cutar.

Ya zuwa karshen ranar Asabar, mutane 26 ne aka tabbatar sun kamu da cutar a yankin musamman na Hong Kong, 10 a yankin Macao sai mutane 17 a yankinTaiwan.

Majinyaci guda daga yankin Macao da wani guda daga yankin Taiwan an sallamesu daga asibiti bayan sun murmure daga cutar. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China