Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan kudin musanya da kasar Sin ta ajiye ya kai fiye da dala trilian 3
2020-02-08 17:51:07        cri
Hukumar kula da ayyuka masu alaka da kudin musanya ta kasar Sin ta sanar a jiya Jumm'a cewa, a watan Janairun bana, kasuwar hada-hadar kudi da ta shafi kudin musanya na kasashe daban daban na gudana yadda ake bukata a kasar, inda ake samun daidaituwa tsakanin yawan kudin musanya da ake samarwa, gami da yawan kudin da ake bukata. Ta yadda aka tabbatar da wani yanayi na samun isassun ajiyar kudin musanya a kasar.

Hukumar ta ce, ya zuwa karshen watan Janairun da ya gabata, yawan kudin musanya da kasar Sin ta ajiye ya kai dalar Amurka trilian 3 da biliyan 115, da kuma miliyan 500, adadin da ya karu da dala biliyan 7.6, ko kuma kashi 0.2%, bisa na karshen watan Disamban bara.

A cewar wani jami'in hukumar, ana ci gaba da fuskantar wani yanayi mai wuya a fannin tattalin arzikin duniya, kana akwai rashin tabbas dangane da kasuwar hada-hadar kudi ta kasa da kasa. Sannan a kasar Sin, annobar Coronavirus ta yi tasiri kan tattalin arzikin kasar, sai dai, tasiri ba mai dadewa ba ne. Ya kuma kara da cewa, yanayin da kasar Sin ke ciki na samun ci gaban tattalin arziki, da karuwa mai inganci bai canza ba. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China