Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Gwamnatin tsakiyar kasar Sin ta kara kai dauki ga lardin Hubei
2020-02-08 18:39:04        cri

Hukumar kula da ayyukan raya tattalin arziki da gudanar da gyare-gyare a kasar Sin, ta sanar a jiya Jumma'a cewa, an kara tura kudi Yuan miliyan 200 (kwatankwacin dalar Amurka miliyan 28.6) ga lardin Hubei, inda aka fi fama da annobar Coronavirus, don taimakawa ayyukan gina dakunan jinya, da sayen wasu muhimman na'urorin, ta yadda za a samar da isashen dauki ga majiyyata, don cimma burin ganin karin majiyyata sun warke.

Ban da haka kuma, hukumar ta yi alkawarin kara zuba kudi don tallafawa aikin samar da wasu kayayyakin da ake bukata don gudanar da ayyukan ceton mutane gami da killace wadanda suka kamu da kwayoyin cutar Coronavirus, tare da jinyarsu, don tabbatar da samun nasara a wannan yakin da ake yi da annobar a kasar. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China