Kwamitin sa ido na Sin zai tura tawaga birnin Wuhan domin binciken batun likita Li Wenliang
Bisa zartaswar kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kwamitin sa ido na kasar Sin zai tura tawagar bincike zuwa birnin Wuhan na lardin Hubei, domin gudanar da bincike a dukkan fannoni, kan batutuwan da jama'ar birnin suka gabatar, masu nasaba da likitin nan mai suna Li Wenliang. (Maryam)
Labarai masu Nasaba