![]() |
|
2020-02-07 10:18:34 cri |
Hukumar ta ce akwai kuma karin wasu sabbin wadanda suka kamu 4,833.
Har ila yau a jiyan, marasa lafiya 962 sun shiga matsanancin yanayi, kuma an sallami mutane 387 daga asibiti, bayan sun warke.
Jimilar wadanda suka kamu da cutar a babban yankin kasar Sin ta kai 31,161 ya zuwa jiya Alhamis, inda kuma jimilar wadanda suka mutu ya kai 636.
Hukumar ta kara da cewa, har yanzu akwai wadanda suka kamu da cutar 4,821 dake cikin matsanancin yanayi, da kuma wasu 26,359 da ake zargin sun kamu.
Ya zuwa jiyan, an tabbatar da mutane 24 sun kamu a yankin musammam na Hong Kong, ciki har da mutum guda da ya mutu, sannan akwai 10 a Macao da 16 a yankin Taiwan. (Fa'iza Mustapha)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China