Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya ta bullo da sabon tsarin biza don saukaka harkokin kasuwanci
2020-02-05 10:01:30        cri

A ranar Talata gwamnatin Najeriya ta kaddamar da sabon tsarin bayar da takardun biza na shekarar 2020 wato (NVP 2020) a takaice, da nufin kyautata muhallin kasuwancin kasar, da janyo hankalin masu zuba jari na kasashen waje, kana da bunkasa fannin yawon bude ido ba tare da lahanta harkokin tsaron kasar ba, shugaban kasar Muhammadu Buhari shi ne ya tabbatar da hakan.

Shugaba Buhari ya ce, daga cikin muhimman batutuwan tsarin, ana fatan sabon tsarin zai taimaka wajen janyo hankalin masu zuba jari a fannin kirkire kirkire, da samar da kwararrun fasahohin masana da kuma ilmi daga kasashen ketare wadanda za su tallafawa ayyukan bunkasa ci gaban kasar.

Shugaban kasar ya ce, aiwatar da sabon tsarin bizar na shekarar 2020 zai taimakawa kasar wajen cimma nasarar yin gogayya a harkokin tattalin arzikin kasa da kasa ta hanyar gina tubalin ci gaban kasar karkashin shirin samar da ingantaccen muhallin kasuwanci na ofishin shugaban kasa.

Sabon tsarin kyautata bizar da Najeriyar wadda daya daga cikin kasashe mafiya karfin tattalin arziki a nahiyar Afrika ta bullo da shi, ya zo ne a daidai lokacin da ake ta kokarin sanya hannu don amincewa da kuma aiwatar da yarjejeniyar kasuwanci maras shinge ta kasashen Afrika, wacce za ta baiwa nahiyar damar yin cudanyar kasuwanci da bunkasa harkokin kasuwanci a tsakanin kasashen nahiyar ta Afrika cikin sauki.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China