Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Mutane 3 sun mutu a hadarin mota a Najeriya
2020-02-04 10:15:52        cri
Wani hadarin mota da ya auku a babbar hanyar motar yankin kudu maso yammacin Najeriya ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 3 da kuma jikkata wasu mutanen 14, kamar yadda wani jami'in dan sandan yankin ya bayyana.

A cewar Babatunde Akinbiyi, kakakin jami'an rundunar kiyaye dokokin tuki ta musamman, ya fadawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, wasu motocin haya biyu ne suka yi karo da juna a babbar hanyar motar Lagos zuwa Ibadan sakamakon matsanancin gudu da kuma tukin ganganci.

Babbar hanyar ita ce wadda ta hada Ibadan babban birnin jihar Oyo dake shiyyar kudu maso yammacin Najeriya da jihar Lagos, birni mafi girma a Najeriya. Kuma ita ce babbar hanyar zuwa yankin arewacin kasar, da kudanci, har ma da gabashin kasar mafi yawan al'umma a nahiyar Afrika.

Akinbiyi ya ce, motocin biyu sun yi karo ne a daidai lokacin da suke tsananin gudu.

Ana yawan samun hadduran motoci a Najeriya, galibi a sanadiyyar daukar kayan da ya wuce kima, ko rashin kyawun hanyoyin mota, ko kuma tukin ganganci.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China