Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Najeriya ta jajantawa kasar Sin game da cutar numfashi da kasar ke fama da ita
2020-02-03 10:11:18        cri

Shugaban tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari, ya mika sakon jimami da fatan alheri ga shugaban kasar Sin Xi Jinping, da daukacin al'ummar Sinawa, a wannan gaba da kasar ke fuskantar yaduwar cutar numfashi ta coronavirus.

Shugaba Buhari ya ce Sin na aiwatar da muhimman matakai na dakile yaduwar wannan cuta, tana kuma hadin gwiwa da kasashen duniya, da hukumomin kasa da kasa wajen cimma nasarar kawar da cutar.

Ya ce ko da yaushe Sin na goyon bayan Najeriya sosai, da ma nahiyar Afirka baki daya, inda a 'yan shekarun nan ma hakan ke kara fadada, don haka abu ne mai muhimmanci ga Sin ta san cewa, Najeriya da daukacin al'ummunta, na tare da ita a wannan lokaci na barkewar cutar coronavirus.

Shugaba Buhari ya ce yana da kwarin gwiwar cewa, Sin za ta shawo kan wannan annoba bisa ingantattun matakai da ake dauka. Daga nan sai ya yi amfani da wannan dama, wajen godewa 'yan kasar sa, bisa karamci da suke nunawa Sinawa mazauna kasar, da ma yadda bullar wannan cuta bai haifar da wata fargaba, ko tashin hankali a sassan kasar ba.

Daga nan sai ya yi addu'ar ganin bayan wannan cuta, da kuma jajantawa wadanda cutar ta hallaka 'yan uwa ko iyalan su. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China