Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kwashe bakin haure 116 daga Libya zuwa Nijer
2020-02-06 11:02:33        cri
Hukumar kula da bakin haure ta kasa da kasa (IOM) ta sanar cewa kimanin bakin haure 116 suka mika wuya don kwashe su daga kasar Libya zuwa Jamhuriyar Nijer.

A cewar hukumar ta IOM, jami'an hukumar sun tallafawa bakin hauren wajen yi musu rijista, da tallafin magunguna da kuma aikin kwashe su.

IOM tana gudanar da aikin sa kai ne karkashin shirin kwashe bakin hauren, inda take daukar nauyin kwashe 'yan ci ranin dake gararamba a kasar Libya don mayar da su kasashensu na asali.

A halin yanzu akwai bakin haure sama da 650,000 dake zaune a kasar Libya, daga cikinsu akwai wasu kimanin 6,000 da ake tsare da su a wasu cibiyoyi, a cewar kididdigar hukumar ta IOM.

Bakin hauren, wadanda galibinsu 'yan kasashen Afrika ne, suna yunkurin tsallaka tekun Mediterranean daga kasar Libya zuwa kasashen Turai sakamakon matsalolin tabarbarewar tsaro da tashe tashen hankula dake cigaba da ta'azzara a kasar ta arewacin Afrika tun daga shekarar 2011, lamarin da ya yi sanadiyyar kifar da gwamnatin shugaban kasar Libya Muammar Gaddafi.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China