Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin tana kokarin gwada wasu magungunan annobar cutar numfashi
2020-02-04 21:20:28        cri
Sun Yanrong, mataimakiyar darekta a sashen kula da halittu na ma'aikatar kimiyya da fasaha ta kasar Sin ta bayyana a yayin taron manem labaru da hukumar kiwon lafiyar kasar Sin ta shirya yau Talata cewa, an samu ci gaba wajen yin nazari kan annobar cutar numfashin da ta bulla a kasar, musamman ma a fannin nazarin magani. Yanzu haka an zabi wasu magungunan yakar annobar, ana nan kokarin gwada su wajen shawo kan annobar da ta bulla. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China