Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ya kamata kasashen duniya su hada kai wajen daidaita matsalar ba-zata da ta shafi lafiyar al'umma
2020-02-04 19:35:56        cri
Yau Talata Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana a nan Beijing cewa, hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta sanar da barkewar annobar cutar numfashi a matsayin lamarin ba-zata da ya shafi lafiyar al'umma, kuma dole ne kasashen duniya su mai da hankali a kai. Dalilin hukumar na daukar wannan mataki, shi ne ba da taimakon da ya wajaba ga kasashen da ba su bullo da ingataccen tsarin da ma isassun kayayyakin kiwon lafiyar al'umma ba. Don haka, kamata ya yi kasashen duniya su hada kai domin daidaita matsalar lafiyar al'umma tare, hakan da ya dace da muradunsu duka.

Madam Hua ta kara da cewa, hukumar WHO ta sanar a ranar 3 ga wata cewa, ban da kasar Sin, akwai mutane 153 da aka tabbatar da suka kamu da annobar cutar numfashi a wasu sassan duniya, wadanda yawansu bai kai kaso 1 cikin dari na jimillar wadanda aka tabbatar da suka kamu da cutar a kasar Sin ba. A shekarar 2009, annobar cutar murar H1N1 da ta barke a kasar Amurka ta yadu a duk duniya har da kasashe da yankuna 214. Sakamakon kokarin da kasar Sin take yi, ya sa annobar cutar numfashi ba ta yadu zuwa sauran kasashe ba. Hukumar WHO ta yaba wa matakan da kasar Sin ta dauka a matsayin sabon abin koyi a fannin yaki da barkewar annobar cuta. Kasar Sin ta fahimci matakan da wasu kasashe suka dauka domin hana yaduwar annobar, amma ta yi fatan cewa, za su kara daukar matakai yadda ya kamata, a magance dakatar da zirga-zirgar mutane. (Tasallah Yuan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China