Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kungiyar ALIPH na fatan Sin ta kara ba gudunmawa wajen kiyaye  abubuwan tarihi a wuraren dake fama da rikice-rikice
2020-01-19 15:15:27        cri

Darektan gudanarwa na kungiyar kiyaye abubuwan tarihi a wuraren dake fuskantar rikice-rikice wato ALIPH Valerie Freland ya shedawa manema labarai kwanan baya a birnin Beijing cewa, a matsayin mambar wannan kungiyar, Sin tana taka muhimmiyar rawa wajen kiyaye abubuwan tarihi a wuraren da ake fama da rikice-rikice, kuma yana fatan kungiyoyin kiyaye abubuwan tarihi daban-daban na Sin za su kara ba da gudunmawa a wannan fanni.

Valerie Freland ya kai ziyara a Beijing da Xi'an daga ranar 12 zuwa 15, a cewarsa, Sin ta mallaki fasahar zamani wajen gyara kayayyakin tagulla, da kayayyakin karau da kayayyakin fadi-ka-mutu da kuma farfado da gine-ginen tarihi, yana sa ran hukumomin kiyaye kayayyakin tarihi da masana na kasar Sin su kara shiga ayyukan a wuraren dake fama da rikice-rikice. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China