Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An kammala gwajin bikin murnar sabuwar shekarar kasar Sin ta 2020 karo na uku
2020-01-19 14:58:05        cri
Jiya Asaba, an kammala gwajin bikin murnar sabuwar shekarar kasar Sin bisa kalandar gargajiya ta shekarar 2020 karo na uku a nan birnin Beijing, wanda babban rukunin gidajen rediyo da telibijin kasar Sin CMG ya gabatar.

Bayan aikin gwaji har sau uku da aka yi, an tsai da shirye-shirye bisa tsari mai kyau, shirye-shirye na kara samun kyautatu.

Bikin da za a gabatar a wannan karo yana mai da hankali sosai kan tuntubar masu kallo.

Wannan biki dai mai sa'o'i 4 dake kunshe da shirye-shirye masu dimbin yawa ya yi amfani da dandali mai kyau, kuma a cikin yanayi mai matukar fari ciki, an gabatar da shirye-shirye masu ban sha'awa dake jawo hankalin jama'a kwarai da gaske, ban da wannan kuma, an yi amfani da fasaha da kimiyya ta zamani don watsa wannan biki ga duk fadin duniya, matakin da ya sa ake sa ran kallon wannan biki kwarai da gaske. (Mai fassarawa: Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China