2020-01-21 20:03:35 cri |
A yau Talata ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana a nan birnin Beijing cewa, asusun lamuni na kasashen duniya IMF, ya fitar da wani rahoto, inda ya daga hasashensa kan karuwar tattalin arzikin kasar Sin, lamarin da ya nuna cewa, kasashen duniya sun amince da ci gaban tattalin arzikin kasar Sin, haka kuma suna cike da imani kan makomar tattalin arzikin kasar.
Rahotanni sun nuna cewa, a jiya Litinin IMF ya fitar da rahoton, inda ya rage hasashensa kan karuwar tattalin arzikin duniya na bana, da badi, zuwa kaso 3.3 da kaso 3.4 bisa dari, amma ya kara hasashensa kan karuwar tattalin arzikin kasar Sin zuwa kaso 6 bisa dari. Game da hakan, Geng Shuang ya yi nuni da cewa, duk da cewa ana fuskantar rikici da kalubale da dama, amma tattalin arzikin kasar Sin ya samu ci gaba cikin lumana, kuma dalilin hakan shi ne, kasar Sin tana da babban karfi a asirce na raya tattalin arzikinta, kuma yanzu haka Sin za ta ci gaba da nacewa ga manufar yin gyare-gyare, tare kuma da daukar matakai a jere, domin tabbatar da saurin ci gaban tattalin arzikin kasar. (Jamila)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China