Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Bin ra'ayin kashin kai da danniya barazana ne ga zaman lafiyar duniya, in ji Wang Yi
2019-12-04 20:38:25        cri
Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ce bin ra'ayin kashin kai, da danniya barazana ne ga zaman lafiya da daidaito a duniya. Wang Yi ya bayyana hakan ne, yayin ganawar sa da takwararsa ta kasar Koriya ta kudu Kang Kyung-wha, lokacin da yake ziyarar aiki yau Laraba a birnin Seoul.

Ya ce bin ra'ayin kashin kai na haifar da illa ga tsarin gudanarwa na kasa da kasa, yana kuma gurgunta tsarin cudanya tsakanin kasashen duniya. Daga nan sai ya jaddada aniyar kasar Sin, ta ci gaba da nacewa akidar cudanya da sauran kasashen duniya bisa salo na zaman lafiya, da yayata akidar daidaito tsakanin kasashe manya da kanana, tare da martaba tsarin dimokaradiyya tsakanin dukkanin kasashen duniya. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China