![]() |
|
2020-01-16 13:40:57 cri |
Tun daga ranar 17 zuwa 18 ga wannan wata, shugaba Xi Jinping zai gudanar da ziyarar aiki a kasar Myanmar. Wannan ne karo na farko da ya ziyarci wata kasar waje a wannan shekara, kana bana shekaru 70 ke nan da kulla dangantakar diplomasiyya a tsakanin Sin da Myanmar.
Taken bayanin da shugaba Xi Jinping ya rubuta a yau shi ne "ci gaba da sada zumunta na 'Paukphaw' a dogon lokaci", inda ya yi nuni da cewa, ya kamata Sin da Myanmar su yi amfani da damar cika shekaru 70 da kulla dangantakar dake tsakaninsu wajen kara yin mu'amala da juna, da zurfafa hadin gwiwarsu a fannonin tattalin arziki da cinikayya, da kara yin hadin gwiwa a harkokin kasa da kasa da yankuna don sa kaimi ga raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu zuwa wani sabon matsayi. (Zainab)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China