Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sakataren MDD ya yi kira da a kara baiwa kasashe masu tasowa taimakon kudi
2020-01-16 09:59:07        cri

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya yi kira ga kasashen duniya, da su taimakawa kasashe masu tasowa, ta hanyar samar musu yanayin da za su ci gajiyar albarkatun dake cikin kasashe da janyo hankulan sassa masu zaman kansu su zuba jari a kasashen.

A jawabin da ya gabatar yayin mika ragamar shugabancin karba-karba na kungiyar G77 da kasar Sin, jami'in na MDD ya yi kira ga dukkan kasashen da suka ci gaba, da su cika alkawuran da suka yi a taron Addis Abba, ciki har da taimakon raya kasa.

A hannu guda kuma ya ce, wajibi ne kasashen duniya, su kara daukar managartan matakan yaki da zurarewar jari, da almundahanar kudade da kaucewa biyan haraji, wadanda ke ci gaba da durkusar da muhimman albarkatun kasashe masu tasowa.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China