Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwamitin sulhu na MDD ya yi tir da harin da aka kai Niger
2020-01-14 09:19:54        cri

Mambobin kwamitin sulhu na MDD sun yi shiru na minti 1 yayin zamansu na jiya Litinin, domin girmama wadanda harin ta'addanci ya rutsa da su a Niger.

Kafin fara zaman da aka saba, jakadan Vietnam Dang Dinh, a matsayinsa na shugaban kwamitin, ya ce kwamitin sulhun na tir da harin ta'addancin da aka kai Niger ranar Alhamis da ta gabata, inda ya bukaci dukkan wadanda ke zauren kwamitin su mike tsaye tare da yin shiru na minti 1 domin sojoji 89 da aka kashe.

Jakadan Niger Abdou Abarry, ya godewa mambobin kwamitin bisa goyon bayan da suka ba kasarsa. Ya kuma godewa ma'aikatan MDD dake kasarsa da kuma kasashe kawayenta. Yana mai cewa, ba don taimakon da suka bayar ba, da adadin wadanda aka rasa ya zarce hakan. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China