Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwamitin sulhun MDD ya gudanar da taruka 258 tare da amincewa da kudurori 52 a 2019
2020-01-14 09:59:11        cri

Wani rahoto da aka wallafa a jiya Litinin ya ce, kwamitin sulhu na MDD ya gudanar da taruka 258 tare da amincewa da kudurori 52, da kuma fitar da sanarwowin shugaba 15 a shekarar 2019.

Kwamitin wanda aikinsa shi ne, tabbatar da tsaro da zaman lafiya tsakanin kasa da kasa, ya yi nazarin ajandu 49 tare da tura tawagogi 5 na dakarun wanzar da zaman lafiya zuwa fagen daga a kasashen Cote d'Ivoire da Guinea Bisssau da yankin Sahel (zuwa kasashen Mali da Burkina Faso) da Iraqi da Kuwait da Colombia da Habasha da Sudan ta Kudu.

Har ila yau, a 2019, kwamitin ya amince da muhimman kudurori 2 dake da alaka da yaki da ta'addanci da suka hada da kuduri mai lamba 2462, wanda ke jadadda bukatar kasashe mambobin MDD su ayyana samar da kudi ga 'yan ta'adda a matsayin laifi da kuduri mai lamba 2482, wanda ke kira ga kasashe mambobin su karfafa tunkarar alakar dake tsakanin ta'addanci a kasa da kasa da kuma manyan laifuffuka.

Rahoton ya kara da cewa, a shekarar 2019, kudurori 42 daga cikin 52 da sanarwowi 11 daga cikin 15, na da alaka yanayin rikici a kasashe ko kuma yankuna, inda jimilar na nahiyar Afrika ya kai 34, adadin da ya dauki kaso 64.2 cikin dari na kudurorin da sanarwowin, sai na yankin gabas ta tsakiya guda 10, kwatankwacin kaso 18.9, yayin da nahiyoyin Asiya da Amurka da Turai, suka samu guda uku-uku, kwatankwacin kaso 5.7 kowannensu. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China