Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Iran na maraba da tsarin da zai ceto yarjejeniyar nukiliyar kasar
2020-01-15 10:20:02        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran Abbas Mousavi, ya sanar a ranar Talata cewa, kasar Iran tana maraba da duk wani matakin da zai iya ceto yarjejeniyar nukiliyar kasar da aka cimma a shekarar 2015.

Mousavi ya ce, a lokutan baya, Iran ta yi kyakkyawan shiri na amincewa da duk wani mataki da zai taimaka wajen ceto muhimmiyar yarjejeniyar ta kasa da kasa, kuma kasar ta goyi bayan duk wani shiri da ya shafi batun yarjejeniyar.

Ya ce a wasu lokuta, Iran ta fayyacewa kowa musamman ga bangarorin kasashen na Turai uku dake da ruwa da tsaki kan yarjejeniyar cewa, idan har aka samu saba alkawari, da mummunar aniya, da kokarin rusa matakan da aka gina, to za ta iya mayar da martani mai tsanani kuma ta hanyar da ya dace.

Kalaman na Mousavi ya kasance martani ne ga yunkurin daidaita rikici na kasashen Birtaniya, Faransa, da Jamus game da yarjejeniyar da aka cimma a shekarar 2015 kan batun nukiliyar Iran.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China