Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Furucin Trump kan Iran ya karfafawa MDD gwiwa
2020-01-09 12:41:13        cri

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres, ya ce ya samu kwarin gwiwa game da furucin baya-baya nan, da shugaban Amurka Donald Trump ya yi game da Iran.

Kakakin sakatre janar din Stephane Dujarric, ya ruwaito shi yana cewa, suna maraba da duk wani furuci dake nuna akwai yiwuwar kaucewa ta'azzarar lamura da fito na fito.

Yayin wani jawabi ta talabijin da aka watsa daga fadar White House, bayan hare-haren makamai masu linzami da Iran ta kaddamar kan sansanonin sojin Amurka, shugaba Trump ya ce zai kara kakabawa Tehran takunkumai, sai dai ba zai ta'azzara tankiyar dake tsakaninsu ba.

Cikin sanarwar da ya fitar jiya, Dujarric ya ce, sakatare janar din zai ci gaba da shiga tsakani.

A ranar Talata ne ma'aikatar tsaron Amurka ta tabbatar da cewa, Iran ta kaddamar da hare-hare da dama kan a kalla sansanoni 2 na sojin kasar da na kawancen kasashe dake Iraqi. Sai dai Trump ya ce babu wanda harin ya rutsa da shi daga bangaren Amurka.

Rundunar sojojin juyin juya hali ta Iraki, ta dauki alhakin kai hare-haren, tana mai cewa, ramuwa ce ga kisan da Amurka ta yi wa janar Qassem Soleimani a Iraki. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China