Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Iraqi ya yi Allah wadai da harin da Iran ta kai kan sansanin sojojin Iraqi
2020-01-09 12:35:49        cri

Shugaban kasar Iraqi Barham Salih, ya yi Allah wadai da harin makamai masu linzami da Iran ta kai kan sansanin sojojin Amurka dake Iraqi.

A wata sanarwar da ta fito daga ofishinsa, Salih ya ce, fadar shugaban kasar ta nuna damuwa game da abin da ya faru, kana ta yi Allah wadai da matakin Iran na kai harin makamai masu linzamin a yankin kasar Iraqin.

A cewar sanarwar, fadar shugaban kasar ta sake nanata kin amincewa da matakin wanda ya saba ikon 'yancin cin gashin kan kasar, da kokarin mayar da Iraqi zuwa wani filin yaki tsakanin bangarorin biyu dake rikici da juna.

Salih ya bukaci bangarorin biyu su kai zuciya nesa kuma su rungumi matakan tattaunawar sulhu domin gujewa barazanar barkewar yaki wanda ka iya lalata zaman lafiya da tsaron yankin har ma da duniya baki daya, in ji sanarwar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China