Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An fara watsa shirin " Bayanan magabata da Xi Jinping yake so" a kasar Myanmar
2020-01-15 09:44:44        cri
An yi bikin kaddamar da shirye-shiryen telabijin masu taken "Bayanan magabata da Xi Jinping yake so", jiya Talata, a birnin Yangon na kasar Myanmar, tare da fara watsa jerin shirye-shiryen a tashar ilimi ta gidan telabijin na Sky Net, wanda shi ne gidan telabijin mai zaman kansa mafi girma a kasar Myanmar. An fara watsa shirin ne daidai kafin ziyarar da shugaba Xi Jinping na kasar Sin zai kai kasar Myanmar.

Babban gidan rediyo da telabijin na kasar Sin CMG ne ya tsara jerin shirye-shiryen "Bayanan magabata da Xi Jinping yake so", inda aka bayyana wasu tsoffin maganganu da labaran tarihi da shugaban na kasar Sin ya taba tsamo su yayin da yake gabatar da jawabai, ko kuma rubuta bayanai. Ta hakan, an nuna yadda shugaba Xi yake fahimtar al'adun gargajiya na kasar Sin, gami da kokarin koyon dabarun mulki daga ciki. (Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China