Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Adadin mutane da suka je yawon shakatawa jihar Xinjiang a shekarar 2019 ya wuce miliyan dari 2
2020-01-13 13:27:40        cri

Kwanan baya, bisa labarin da aka samu daga taron zagaye na uku na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 13 na yanki mai cin gashin kansa na Uygur na jihar Xinjiang, an ce, a shekarar 2019, adadin mutane da suka je yawon shakatawa jihar Xinjiang ya wuce miliyan dari 2, adadin da ya karu da 41.6%, kuma, jihar ta sami kudin shiga na yawon shakatawa Yuan biliyan dari uku da arba'in da biyar da miliyan dari biyu da sittin da biyar, wanda ya karu da 40.4%.

A shekarar da ta gabata, jihar Xinjiang ta mai da hankali kan raya harkokin yawon shakatawa a fadin jihar, da kuma hada harkokin yawon shakatawa da al'adu waje guda, domin inganta ayyukan ba da hidima. A sanadin haka, yawon shakatawa a lokacin kankara da yawon shakatawa na tuka mota da kai sun sami bunkasuwa cikin sauri a jihar. Kuma bunkasuwar harkokin yawon shakatawa ta ba da taimako ga bunkasuwar sana'ar samar da abinci da sana'ar masaukan baki da sauransu, ta kuma samar da karin guraben aikin yi. A halin yanzu, sana'ar yawon shakatawa ta zama sana'ar dake kara kudin shiga ga al'ummar jihar Xinjiang.

Haka zalika, bayanai na nuna cewa, a shekarar 2020, gwamnatin jihar Xinjiang za ta goyi bayan kamfanonin kasar wajen habaka kasuwannin yawon shakatawa, domin samun karuwar masu yawon shakatawa, ta yadda adadin zai wuce miliyan dari 3. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China