Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wakilin MDD ya yi gargadi game da yawaitar hare haren ta'addanci a yammacin Afrika da Sahel
2020-01-09 10:19:21        cri

Wakilin MDD a yammacin Afrika da yankin Sahel ya ja hankalin kasa da kasa game da yawaitar hare haren ta'addanci kan fararen hula da sojoji a shiyyar tun daga watan Yulin bara.

Mohamed Ibn Chambas, shugaban ofishin MDD mai kula da yammacin Afrika da yankin Sahel, ya fadawa taron kwamitin sulhun MDD cewa, yammacin Afrika da yankin Sahel suna fuskantar munanan hare haren ta'addancin a watannin baya bayan nan.

Game da kasashen Burkina Faso, Mali da Nijer, ya ce, adadin wadanda hare haren ta'addancin ya yi sanadiyyar rayukansu ya ninka sau biyar tun daga shekarar 2016, inda aka samu hasarar rayuka sama da 4,000 a shekarar 2019 kadai, idan an kwatanta da mutuwar mutane 770 a shekarar 2016.

Ya kara da cewa, wuraren da hare haren ta'addancin suka fi mayar da hankali sun koma shiyyar gabashi daga Mali zuwa Burkina Faso kuma barazanar tana ci gaba da karuwa a kasashen yammacin Afrika a jihohin dake gabar teku, kuma yawan mutanen da aka hallaka a Burkina Faso ya karu daga mutane 80 a shekarar 2016 zuwa sama da mutane 1,800 a shekarar 2019.

Wakilin MDDr ya ce ayyukan ta'addanci, da hare haren 'yan bindiga, da rikicin kabilanci duka suna da alaka da juna, ya nanata cewa galibi a irin wadannan yankuna marasa galihu masu tsattsauran ra'ayi suna amfani da wannan damar wajen ba da kariya ga mazauna yankunan domin samun hadin kansu.

Haka zalika, ya jaddada cewa tilas ne ayyukan yaki da ta'addanci ya mayar da hankali wajen neman goyon bayan al'ummomi mazauna yankunan da matsalar ta shafa.

Kana ya bukaci shugabannin shiyyoyin da su cika alkawurran da suka dauka tare da hadin gwiwar abokan hulda na kasa da kasa don bayar da cikakken goyon baya wajen aiwatar da dabarun yaki da ayyukan ta'addanci a shiyyar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China