Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ziyarar Wang Yi ta farkon shekara na jaddada martaba abotar Sin da Afirka
2020-01-08 14:27:55        cri

Sanin kowa ne cewa, ziyarar da ministan harkokin wajen kasar Sin ke kaiwa wasu kasashen Afirka, a duk farkon shekara, ta zama wata al'ada da kasar Sin ta dade tana rayawa. A bana kuma wannan al'ada ke cika shekaru 30 da kafuwa.

A wannan karo, ministan harkokin wajen Sin, kuma dan majalissar gudanarwar kasar Wang Yi, ya fara ziyarar ne a kasashen Masar da Djibouti, da Eritrea, da Burundi da kuma Zimbabwe tun daga jiya Talata, ziyarar dake dada haskaka irin muhimmanci da Sin ke dorawa ga kyakkyawan kawancen ta da kasashen nahiyar Afirka, da ma abota mai inganci dake tsakanin sassan biyu.

Sin da kasashen Afirka sun kasance 'yan uwa, kuma abokan hulda na hakika, inda suke marawa juna baya, cikin yanayin walwala da lokutan kunci. Tun cikin shekarun 1950 da 1960, yayin da jamhuriyar jama'ar kasar Sin ke fama da tarin kalubale, kasar ke ci gaba da mara baya ga kasashen Afirka, a kokarin su na samun 'yanci da dogaro da kai. A shekarar 1971, Sin ta sake karbar matsayin ta na kasa mai kujera a MDD, da tallafin 'yan uwa na nahiyar Afirka, wadanda suka baiwa Sin din cikakken goyon baya.

A watan Janairun shekarar 1991, a gabar da duniya ke fama da manyan sauye sauye bayan kammalar yakin cacar baka, ministan harkokin wajen Sin na wancan lokaci Qian Qichen, ya ziyarci kasashen Habasha da Uganda, da Kenya da Tanzania, ziyarar da ta aza tubulin wannan al'ada ta ziyartar nahiyar Afirka a farkon duk shekara, ga ministocin harkokin wajen Sin da suka biyo bayan sa.

Cikin shekaru kusan 30 da suka shude, hadin gwiwar Sin da kasashen nahiyar Afirka na kara zurfafa, inda a farkon shekarun 1990, Sin da Afirka suka karkata alakar su zuwa sassan gwamnatoci. A daya hannun kuma, yayin da Sin ke ci gaba da aiwatar da manufar nan ta yin gyare gyare a cikin gida, wasu sassan 'yan kasuwar Sin sun fara karkata ga Afirka wajen zuba jari.

A shekara ta 2000, aka kafa dandalin tattauna hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen nahiyar Afirka ko FOCAC a takaice, a wani mataki na bunkasa tuntuba tsakanin sassan biyu cikin daidaito da samun moriyar juna. Wannan dandali ya bude sabon shafin inganta hadin gwiwa, da kawance tsakanin Sin da kasashen Afirka.

Yayin taron kolin FOCAC da ya gudana a birnin Beijing a shekarar 2006 ga misali, an cimma wata gagarumar nasara a tarihin alakar Sin da kasashen Afirka, domin kuwa a wannan taro ne aka daga matsayin kawance Sin da Afirka, zuwa cikakken hadin kai mai kunshe da daidaito a fannin siyasa da martaba juna, da bunkasa hadin gwiwar tattalin arziki na cin moriyar juna, da musayar al'adu.

Kaza lika an ayyana daukar wasu matakai guda 8, domin bunkasa hadin gwiwar sassan biyu, ciki kuwa hadda kafa asusun bunkasa ci gaban Sin da Afirka, da kafa yankunan cinikayyar kasashen waje da hadin gwiwar tattalin arziki a Afirka.

Yayin da ake kara samun ci gaba karkashin wannan hadin gwiwa, taron kolin FOCAC na birnin Johannesburg a shekarar 2015, da ma wanda ya gudana a birnin Beijing cikin shekarar 2018, dukkanin su sun shaida irin ci gaban da ake samu a fannin raya masana'antu a Afirka. Hakika dukkanin wadannan tsare tsare da ake aiwatarwa, sun haifar da da mai ido ga miliyoyin al'ummun nahiyar Afirka.

Har kullum Sin na daukar Afirka da muhimmanci. Ko da ma a shekarar 2013, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya zabi nahiyar a matsayin yanki na farko da zai ziyarta, a jerin ziyarar da zai gudanar a kasashen ketare, bayan da ya hau karagar mulki. Shugaban ya gabatar da kudurorin aiwatar da komai bisa gaskiya, da cimma sakamako, da rungumar akidun kaunar juna da Imani da juna, da maida hankali ga cimma manyan nasarori da cin moriya tare, karkashin alakar sassan biyu.

Shugaba Xi ya sha alwashin ganin Sin ta ci gaba da zama abokiyar dogaro, kuma kawa ta hakika ga nahiyar Afirka, wadda kuma za ta karfafa ci gaban dangantakar ta da kasashen nahiyar.

A matsayin Sin na kasa mai tasowa mafi girma, yayin da Afirka ke matsayin nahiya mai tasowa mafi girma, sassan biyu sun jima suna rike da kudurorin cin moriya tare, da cin gajiya daga juna, sun kuma zama kyakkyawan misali na irin kyakkyawan kawancen dake gudana tsakanin kasashe masu tasowa. Yawan kudaden da fannin cinikayayyar sassan biyu ya kunsa ya karu, daga dalar Amurka biliyan 10.6 a shekara ta 2000 zuwa dala biliyan 204.2 a shekara ta 2018.

Yayin da hadin gwiwar sassan biyu ke kara fadada, nahiyar Afirka na kara sauyawa, zuwa nahiya mai karsashin samun ci gaba. Shawarar nan ta "Ziri daya da hanya daya" wadda Sin ta gabatar a shekarar 2013, ta zamo wani karfi dake ingiza hadin gwiwar sassan biyu, ta kuma samu karbuwa daga sama da kasashen Afirka 40.

Da kakkarfan goyon bayan jari, da fasahohi da kwararru na Sin, kasashen Afirka da dama sun samu gagarumin ci gaba ta fuskar ababen more rayuwa. Karkashin irin wannan ci gaba, kasashen da ba su da makwaftaka da teku kamar Botswana, da Zambia da sauran su, sun sadu da yankunan teku, wanda hakan ya kara dunkule sassan nahiyar wuri guda.

A kasashen dake gabashin nahiyar Afirka kuwa, Sin ta taimaka wajen gina layin dogo da ya hade biranen Mombasa da Nairobi, da layin dogon Habasha zuwa Djibouti, wanda shi ma ya sauya yanayin ci gaban wannan yanki.

A yanzu haka kuwa, an kafa yankin cinikayya maras shinge na Afirka, wanda ya kunshi mutanen da yawan su ya kai biliyan 1.2, yayin da Afirka ke kan wata gaba ta sauya akalar ci gaban ta. Ana dai iya cewa, an kai wata gaba mafi dacewa, ta hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka a fannin raya shawarar "ziri daya da hanya daya", shawarar da ke da kusanci ta fuskar ma'ana, da kudurorin ci gaba na kungiyar tarayyar Afirka, na nan da shekarar 2063, da ma kudurorin ci gaba mai dorewa na MDD, na nan da shekarar 2030, da kuma tsare tsaren ci gaba na bai daya da nahiyar Afirka ke fatan cimmawa.

A bana ne dai ake cika shekaru 20 da kaddamar da dandalin FOCAC, kana shekaru 60 na bikin 'yancin kan Afirka. A nata bangare, kasar Sin na daf da cimma burin ta na samar da al'umma mai matsakaiciyar wadata a dukkanin fannoni, da kuma cimma burin kawar da talauci tsakankanin al'ummar ta.

Ana sa ran ziyarar Mr. Wang a Afirka, a kuma farkon wannan shekara, za ta kara karsashin hadin gwiwar sassan biyu, ta kuma daga matsayin dangantakar su zuwa wani sabon matsayi na ci gaba.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China