Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin na fatan za a kai zuciya nesa domin kaucewa tsanantar yanayi a yankin Gulf
2020-01-03 20:17:55        cri

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Geng Shuang, ya ce Sin na fatan dukkanin sassa masu ruwa da tsaki, a takaddamar da ta kunno kai a yankin Gulf musamman Amurka, za su kai zuciya nesa, su kuma kauracewa aiwatar da matakan da ka iya kara rura wutar rikici a yankin.

Kalaman na Geng Shuang, na zuwa ne bayan da aka tabbatar da rasuwar wani kwamanda a rundunar da ke samun goyon bayan kasar Iran, wato Manjo Janar Qassem Soleimani, sakamakon wani hari ta sama da ya auku a filin jirgin saman birnin Bagadaza. Tuni dai ma'aikatar tsaron Amurka ta tabbatar da cewa, ita ce ta aiwatar da harin na "kare kai", wanda ya hallaka kwamanda Soleimani.

To sai dai a cewar Mr. Geng Shuang, har kullum Sin na adawa da amfani da karfin tuwo, yayin duk wata takaddama ta kasa da kasa, tana mai fatan dukkanin sassa, za su rungumi ka'idojin da MDD ta shimfida, da sauran kudurori na alakar kasa da kasa wajen cimma maslaha. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China