Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Amurka za ta tura sojoji 750 zuwa yankin Gabas ta Tsakiya
2020-01-01 15:55:19        cri

Sakataren harkokin tsaron Amurka, Mark Esper, ya bayyana cewa, kasarsa za ta tura kimanin sojoji 750 nan take, zuwa yankin Gabas ta Tsakiya, matakin da aka dauka sa'o'i bayan masu zanga-zanga sun kuntsa ofishin jakadancin kasar dake birnin Baghdad na Iraqi.

Cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na tweeter da yammacin jiya, Mark Esper ya ce za a tura sojoji kimanin 750 nan take zuwa yankin, sannan ana shirin tura karin wasu sojojin kai daukin gaggawa cikin wasu kwanaki masu zuwa.

Ya ce tura sojojin mataki ne da ya dace kuma shiri ne na tunkarar abun da ka-je-ya-zo, la'akari da karuwar barazana ga jami'ai da ofisoshin Amurka, kamar abun da ya faru a Baghdad.

Matakin na ma'aikatar tsaron Amurka wato Pentagon, ya zo ne sa'o'i bayan daruruwan masu zanga-zanga, dake makokin mambobin kungiyar Hashd Shaabi da harin Amurka a Iraqi ya yi sanadin mutuwarsu, suka farwa ofishin jakadancin kasar dake Baghdad.

Galibin masu zanga-zangar sanye cikin kakin Hasd Shaabi, sun taru a gaban ofishin jakadancin suna masu furta kalaman soka ga luguden wutar da dakarun Amurka suka yi kan sansanonin kungiyar.

Wani jami'in ma'aikatar harkokin wajen Iraqi da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaidawa Xinhua cewa, daga bisani zanga-zangar ta rikide zuwa rikici, inda masu zanga-zangar suka kona hasumiyar gadi da kofar ofishin jakadancin na waje.

Shugaban Amurka Donald Trump, ya dora laifin kan Iran, yana mai cewa ita ta kitsa harin. Cikin sakon da ya wallafa a shafin tweeter daga bisani, ya yi barazanar dora alhakin rayukan da aka rasa ko asarar da aka yi a duk wani ofishin Amurka a kan kasar Iran. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China