Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Trump ya yi barazanar karawa Iran takunkumi
2019-07-11 09:46:05        cri

A jiya Laraba ne shugaban Amurka Donald Trump, ya sake yin barazanar kakabawa kasar Iran sabon takunkumi, a gabar da dangantakar kasashen biyu ke kara tsami.

A wani sako da ya rubuta a shafin sa na Tweeter, shugaban na Amurka ya ce "Iran ta jima tana sarrafa sinadaran nukiliya a boye, wanda hakan ya sabawa mummunar yarjejeniyar nan da ta shafi kudade da yawan su ya kai dala biliyan 150, da tsaffin gwamnatocin John Kerry da Obama suka amincewa.

Ya ce kowa ya san cewa, nan da 'yan shekaru, wannan yarjejeniya za ta kawo karshe. Don haka ba tare da bata wani lokaci ba, za a karawa Iran sabbin takunkumai.

Kalaman na shugaba Trump dai na zuwa ne, 'yan kwanaki bayan da kasar ta Iran ta bayyana cewa, ta fadada matakin tace sinadarin uranium da take sarrafawa daga kaso 3.67 zuwa 4.5 bisa dari, sama da matakin da yarjejeniyar nukiliyar kasar ta shekarar 2015 ta tanada.

Jim kadan da fitar wannan sanarwa ne kuma, mataimakin shugaban Amurka Mike Pence, tare da sauran manyan kusoshin gwamnatin sa, suka sha alwashin karawa Iran din matsin lamba ta fannin tattalin arziki.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China