Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Wani asibiti a Nijeriya ya raba wasu tagwaye da aka haifa manne da juna
2020-01-09 09:49:33        cri

Wani asibiti a Nijeriya, ya tabbaatar da nasarar raba wasu tagwaye mata, da aka haife su manne da juna, bayan aiwatar da tiyata sau da dama.

Jaf Mommoh, shugaban babban asibitin birnin Abuja wato National Hospital, ya shaidawa manema labarai cewa, tagwayen sun manne da juna ne a kirji da ciki.

Ya ce an haifi tagwayen ne a asibitin gwamnatin tarayya dake jihar Nassarawa dake arewacin kasar a ranar 13 ga watan Agustan 2018, inda daga baya aka tura su asibitinsa domin a raba su.

Likitan ya alakanta nasarar da aka samu da tawagar ma'aikatan lafiya ta asibitin, da isassun kudi da kuma ammanar da iyayen tagwayen suka yi da asibitin.

Ya kuma yi kira ga gwamnatocin jihohi, su kara zuba kudi ga bangaren kiwon lafiya, wanda zai taimaka wajen magance irin wannan kalubalen lafiya da inganta bangaren amfani da kwararrun da ake da su da kuma tabbatar da asibitoci na da fannin kwarewa na musammam.

A nasa bangaren, shugaban tawagar likitocin da suka raba tagwayen, Emmanuel Ameh, ya ce aikin tiyatar ya dauki sama da sa'o'i 12, sannan ya kunshi ma'aikatan lafiya 78. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China