Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Za a mayar da 'yan gudun hijirar Kamaru dake Najeriya gida
2020-01-01 14:46:41        cri

Ministan ma'aikatar dake lura da yankunan kasar Kamaru Paul Atanga Nji, ya ce nan gaba kadan, za a kwashe 'yan kasar Kamaru su kimanin 700 dake zaune a Najeriya zuwa gida.

Tun a ranar Talatar makon jiya ne dai kashin farko na 'yan gudun hijirar Kamarun suka isa gida. Cikin wannan rukuni kuwa hadda mutane 87, mambobin kungiyar 'yan awaren kasar Kamaru, da jagororin su Janar Nambere da Janar Nkongho, wadanda tuni suka mika makaman su.

Da yake tsokaci ga manema labarai game da komawar ta su gida, jim kadan bayan saukar su a filin jirgin sama na Nsimalen dake birnin Yaounde, Janar Nkongho, ya ce "dole mu dawo gida, muna kuma fatan za a yi mana afuwa."

Shi ma a nasa bangare Janar Nambere cewa ya yi, "A gani na lokaci ya yi da sauran al'ummar kasar Kamaru za su yi watsi da tashin hankali."

Alkaluman MDD sun nuna cewa, ya zuwa watan Yulin shekarar 2019 da ta gabata, akwai kusan 'yan Kamaru 40,000 dake samun mafaka a Najeriya, sakamakon tashe tashen hankula masu nasaba da dauki ba dadi, tsakanin dakarun 'yan tawayen kasar ta Kamaru, da jami'an tsaron kasar, a yankuna biyu na kasar dake magana da Turancin Ingilishi.(Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China