Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yan bindiga sun kashe mutane 19 a yankin tsakiyar Nijeriya
2020-01-04 15:49:35        cri

Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta tabbatar da cewa, wani hari cikin dare, da wasu 'yan bindiga suka kai yankin tsakiyar kasar, ya yi sanadin mutuwar mutane 19.

An kuma kone gidaje da dama, ciki har da wasu wuraren ibada da fadar sarkin garin, yayin harin da aka kai ranar Alhamis da daddare a garin Tawari na jihar Kogi, dake yankin tsakiyar kasar.

Kakakin 'yan sandan jihar Kogi, Williams Anya, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, maharan sun shiga garin ne a kan babura. Garin Tawari na da nisan kilomita kalilan daga garin Gegu, a kan babbar hanyar Lokoja zuwa Abuja, babban birnin kasar.

Williams Anya, ya ce an tura karin 'yan sanda yankin, domin dakile maimatuwar harin.

Wani mazaunin kauyen mai suna Ikeleji, ya ce 'yan bidinga sama da 100 ne suka farwa kauyen. Kuma harin ya shafe lokaci mai tsawo har zuwa asubahin ranar Juma'a, inda maharan suka rika shiga wasu zababbun gidaje suna kwashe kayayyakin abinci da kuma lalata kadarori.

Kakakin 'yan sandan ya ce, wannan ne karon farko da aka kai wani hari garin.

A jawabin da ya yi dangane da lamarin, cikin wata sanarwa da aka fitar, gwamnan jihar, Yahaya Bello, ya soki harin da ya kira na rashin imani, tare da umartar hukumomin tsaro su farauto maharan. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China