Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rundunar sojojin Najeriya ta ba da tabbacin harin da Boko Haram ta kaiwa kwamandojinta
2020-01-08 09:56:18        cri

Mayakan Boko Haram masu yawa aka hallaka a wani musayar wuta da aka yi bayan bude wutar da aka yiwa manyan kwamandojin sojojin Najeriya a jihar Borno dake shiyyar arewa maso gabashin kasar.

Akwai a kalla kwamandojin sojoji 4 masu yaki da mayakan Boko Haram a shiyyar arewacin Najeriyar cikin ayarin da 'yan ta'addan suka kaiwa harin a karamar hukumar Kaga dake jihar Borno a ranar Litinin, in ji rundunar sojojin.

Manjo janar Olusegun Adeniyi, kwamandan rundunar sojoji ta musamman dake shiyyar arewa maso gabashin kasar, da sauran kwamandojin sojoji uku suna kan hanyarsu ne daga sansanin sojojin dake garin Jakana a jihar Borno, a lokacin da mayakan na Boko Haram suka yi arangama da sojojin daga cikin daji, Aminu Iliyasu, kakakin rundunar sojoji a yankin ya shedawa manema labarai.

A cewar Iliyasu, harin ya biyo bayan burin da mayakan Boko Haram ke da shi na yin ramuwar gayya kan wasu haren haren da sojojin kasar suka kaddamar ne inda suka hallaka manyan kwamandojojin Boko Haram a ranar 6 ga watan Disambar bara.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China