Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yan sandan Najeriya sun dakile yunkurin fashin banki a Abuja
2019-12-29 15:06:31        cri

A jiya Asabar 'yan sandan Najeriya sun yi nasarar dakile yunkurin fashin banki a wani yankin Abuja, babban birnin kasar ta yammacin Afrika, kana sun yi nasarar kashe mutum guda cikin 'yan fashin, sannan sun kama sauran 'yan fashin hudu.

Bala Ciroma, kwamishinan 'yan sandan birnin Abuja, ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na Xinhua faruwar lamarin, ya ce jami'an 'yan sandan sun yi nasarar kashe guda daga cikin 'yan fashin, sannan sun damke ragowar mutane 4 a lokacin da jami'an suka kai farmaki kan barayin.

Ya kara da cewa, "Fashin banki ne wanda bai samu nasara ba. Mun hana 'yan fashin yin sata a bankin" in ji Ciroma.

Wasu shaidun gani da ido sun fadawa Xinhua cewa, 'yan fashin sun shiga cikin bankin ne da safiyar ranar Asabar, kuma sun makale a cikin ginin bankin har tsawon wasu sa'o'I, sannan 'yan sanda suka yiwa ginin bankin kawanya.

Hukumar 'yan sandan ta ce, komai ya daidaita bayan da jami'an tsaro suka yi hadin gwiwar tabbatar da tsaron yankin.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China