Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sojojin Kamaru sun ce fashewar gurneti bisa kuskure ya kashe mutane 9 a kan iyakar arewacin kasar
2020-01-08 09:29:10        cri

Rundunar sojojin Kamaru ta ce an samu fashewar gurneti bisa kuskure a ranar Litinin a yankin arewacin kasar dake makwabtaka da Najeriya, sabanin harin kunar bakin wake.

A cewar kakakin rundunar sojojin Kamaru, Kanal Cyrille Atonfack Nguemo, mutane 9 ne suka mutu kana wasu mutanen 26 sun samu raunuka a lokacin da gurnetin ya tarwatse da yammacin ranar Litinin a kan gadar kogin El Beid dake garin Fotokol a Kamaru. Fashewar ta faru ne sakamakon sakaci wajen kula da gurnetin wanda wasu kananan yara su biyu suka tsinta a cikin yashi a yankin.

Rahotannin farko sun nuna cewa mutane 11 ne suka mutu kana wasu 26 kuma sun samu raunuka a sakamakon fashewar wanda aka yi amanna harin kunar bakin wake ne da mayakan Boko Haram suka kaddamar.

Sai dai Nguemo ya ce, bisa binciken da aka gudanar da kuma shaidun ganin da ido sun tabbatar da cewa ba harin kunar bakin wake ba ne.

Mutanen 9 da suka mutu dukkansu 'yan Najeriya ne, sannan wasu 'yan Najeriyar 21 sun jikkata gami da wasu mutanen 5 'yan Kamaru sun samu raunuka a sanadiyyar fashewar.

An garzaya da dukkan mutanen da suka ji raunin zuwa asibitoci a garin Fotokol.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China